Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Raba Gardama Ya Janyo Gardama A Tsakanin Masu Kallon Shirin “Labarina”


Shirin "Labarina" na kamfanin Saira Movies (Facebook/Aminu Saira)
Shirin "Labarina" na kamfanin Saira Movies (Facebook/Aminu Saira)

Wani abu da masu kallo za su tsaya su gani shi ne, shin Raba Gardama zai iya takawa Presdo birki?

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kamfanin Saira Movies ya dawo da fitaccen shirinsa na “Labarina” zango na bakwai.

Labarin ya ta’allaka ne kan Sumayya (Fati Washa) wacce maza da dama suke mutuwar sonta.

Daga cikin mazajen da suke sonta, akwai Mahmud (Nuhu Abdullahi,) wanda ga dukkan alamu ya riga ya mutu – wanda shi kuma ta fi so, akwai kuma Lukman (Yusuf Saseen) wanda hankalinta ba ya kansa.

Fati Washa (Sumayya) Hoto - Instagram/Fati Washa
Fati Washa (Sumayya) Hoto - Instagram/Fati Washa

Sai uwa uba – Presdo (Isah Ferozkan) mai fama da lalurar kwakwalwa, kuma mai mummunan fushi a duk lokacin da ransa ya baci.

Ya kan iya aiwatar da komai idan ransa ya baci – har da kisa. Kuma da shi aka yi musu baiko.

An kammala zango na shida ne yayin da ake ta kai ruwa rana kan wani mutum na hudu da ya ki bayyana kansa, amma yake yi wa kansa inkiya da “Raba Gardama.”

Raba Gardama mutum ne mai arziki mai kafa a ko’ina, ta yadda babu inda zai je neman alfarma ba a yi masa ba.

Haka ya yi ta yawo da hankalin Sumayya yana aika mata da kyaututtuka da nema mata alfarma – ciki har da sa hannu a saki mahaifinta daga hannun hukuma saboda wani gagarumin laifi da ya yi a baya.

Isah Ferozkhan (Presdo) (Hoto: Facebook/Isah Ferozkhan)
Isah Ferozkhan (Presdo) (Hoto: Facebook/Isah Ferozkhan)

Duk da yake, ya dauki tsawon lokaci yana boye kansa, yanayin takun farko da Raba y yi har ya sa Sumayya ta yi zaton ko Mahmud ne – amma kuma Mahmud ya riga ya mutu.

Abubuwa sun kara rincabewa, bayan da Presdo ya gano wani mai suna Raba Gardama na bibiyar matar da zai aura.

An kwashe kusan daukacin zango na shida Presdo wanda ke mutuwar son Sumayya, da ita kanta Sumayyar da ahalinta, suna ta kokarin gano wane ne Raba Gardama.

Kwatsam sai dubun Hajara (Hajara Isah) daya daga cikin kawayen Sumayya ya cika bayan da aka kama ta tana waya da Raba-Gardama kuma Presdo yana wajen. Anan zango na shida ya kare.

Hajara Isah, Hajara (Instagram/Hajara Isah)
Hajara Isah, Hajara (Instagram/Hajara Isah)

Yayin da aka dawo zango na bakwai, ba zato ba tsammani sai darektan Labarina Malam Aminu Saira ya yanke shawarar bayyanawa masu kallo Adam Garba a matsayin Raba-Gardama.

Adam Garba sabon jarumi ne da tauraruwarsa ke haskwa a fagen shirya fina-finan Hausa.

Koda yake, ya yi fina-finai da dama ciki har da na kudancin Najeriya, amma ba duka masu bibiyar fina-finan Kannywood ne suka san shi ba.

Hasali ma za a iya cewa, fim din Kwana Casa’in mai dogon zango da Arewa 24 ke nunawa ne y fito da shi idon jama'a.

Sai dai gabatar da shi a matsayin Raba Gardam da Saira ya yi a shirin Labarina, ya raba kawunan masu bibiyar shirin kan dacewa sa ko akasin haka musamman a shafukan sada zumunta.

“Ko kaɗan ban ji haushin Aminu Saira ko ganin rashin dacewar wanda ya saka a matsayin Raba-gardama ba. Domin hakan da ya yi shi ne daidai.” In ji Mohammed Bala Garba, Maiduguri.

Yusuf Saseen, Lukman (Instagram/Yusuf Saseen)
Yusuf Saseen, Lukman (Instagram/Yusuf Saseen)

Ya kara da cewa, “ko kaɗan ban ji haushin Aminu Saira ko ganin rashin dacewar wanda ya saka a matsayin Raba-gardama ba. Domin hakan da ya yi shi ne daidai.”

“Gaskiya role din bai dace da shi ba ko kadan, Aminu Saira da Ali Nuhu ya kawo, ya fi dacewa da role din wallahi.” Zailani Abubakar ya ce a shafin Facebook.

“Mu dai a matsayinmu na ‘yan kallo hakan bai mana dadi sam, sam.” Yunusa Adamu Idris ya ce.”

“Na yaba matsayin da fito, a kamili, dan sarauta, marar girman kai, Almajiri kuma mai tauhidi. Hakan tabbas ya burge ni.” In ji Rufai Habu Bille.

Duba da yadda muhawara ta kaure tun bayan nuna Raba Gardama, Malam Saira bai yi wata-wata ba, ya mayar da martani inda ya ce har istihara sai da ya yi kafin a zabi Adam Garba.

A wata hira da ya yi wacce ta karade shafukan sada zumunta, Saira ya ce an kai ruwa rana kafin su kai ga zabin Adam Garba a matsayin raba-gardama.

Malam Aminu Saira, Darektan Shirin Labarina kuma shugaban kamfanin Saira Movies (Hoto: Instagram/Aminu Saira)
Malam Aminu Saira, Darektan Shirin Labarina kuma shugaban kamfanin Saira Movies (Hoto: Instagram/Aminu Saira)

“Mutane da yawa mun zauna mun yi debate (muhawara) sosai akan wannan character (dan wasa) ta raba gardama. Mutane sun tsammanin z a dakko wani Jarumi ne wanda yake sananne a sa.” Saira ya ce.

“Wallahi na yi Istihara ban san adadi ba. Allah zaba mana wanda zai yi fiye da abin da muke tsammani. Wallahi ina zaune aka kawo na dudduba clips dinsa na ga ya yi.”

“A cikin mutane (jarumai) top three (manya uku) da na taba aiki da su a duniya suka ba ni mamaki ta fuskar baiwa, wallahi wannan raba gardamar na ciki. Wallahi ba ya wuce minti uku zuwa biyar zai dauke dauke script din da aka ba shi.

Tun bayan da da Malam Saira ya fito ya yi magana, akwai alamu da ke nuna an yayyafawa lamarin ruwan sanyi.

Yanzu kuma ‘yan kallo za su zuba ido su ga ya irin rawar da Adam Garba zai taka a shirin na Labarina.

Wani abu da masu kallo za su tsaya su gani shi ne, shin Raba Gardama zai iya takawa Presdo birki?

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG