No media source currently available
Kimanin mutane miliyan biyar ne suka yi fama da malaria a 2022 a Kenya kuma daga ciki, mutane 12,000 suka mutu, a cewar hukumar lafiya ta duniya. Akasarin wadanda abin ya shafa yara ne da mata masu juna biyu. Yanzu an dan samu ci gaba bayan da aka samu damar sarrafa maganin cutar malaria a kasar.
Wace damuwa kuke da ita a game da Tarin Fuka? Shina an taba muku gwajin cutar TB ko kuma wasu na kusa da ku? Ga abinda wasu ‘yan Najeriya suke bayyanawa.
Mireille Kamariza, kwarariya ce a fannin kimiyyar kwayoyin hallitar dan Adam a Jami’ar California na birnin Los Angeles, ta bullo da wani tsarin gwaji da zai iya gano kwayar bakteriya cikin sauri, ba tare da kuskure ba kuma mai rahusa.
Shin ya ya girman kalubalen yaki da wannan cuta ta Tarin Fuka ya ke, musanman a Najeriya. Kuma wadanne hanyoyi mutane za su bi don kare kai daga cutar? Hussaina Mohammed ta tattauna da Dr. Goni Imam Ali, jami’in shirin yaki da cutar tarin fuka da kuturta a jihar Borno.