No media source currently available
A farkon wannan shekarar, kungiyar dake fafutukar yaki da cin hanci ta kasa da kasa, Transparency International, cikin rahotonta na 2023, ta ce yaki da matsalar cin hanci da rashawa a Afirka ya fuskanci koma-baya sosai, inda a wasu kasashen, babu wani abu da aka cimma a game da haka.
Hukumomi a Najeriya su na duba yiwuwar bullo da jami’an ‘yan sanda mallakin jihohi a fadin kasar a wani bangare na magance hare-haren ‘yan bindiga, da garkuwa da mutane da kuma ‘yan fashin daji. ‘Yan Najeriya dai sun yi maraba da wannan yunkuri, sai dai suna cike da shakku.
Kungiyar ta Transparency International ta ce matsalar cin hanci a bangaren shari’a ya na ci gaba da yin mummunar illa ga marasa galihu. A game da girman wannan matsala, mun tattauna da Auwal Musa Rafsanjani, Daraktan kungiyar ta Transparency International a Najeriya.