Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Shadda Ya Samu Lambar Yabo A Bikin MVCA

Bashir Mai Shadda bayan da ya karbi lambar yabo a bikin MVCA a Legas (Instagram/Bashir Mai Shadda)
Bashir Mai Shadda bayan da ya karbi lambar yabo a bikin MVCA a Legas (Instagram/Bashir Mai Shadda)

Mai Shadda ya lashe lambar yabon ce da fim din “Aisha” a rukunin fina-finan da ake shiryawa da harsunan cikin gida wanda Hausa na ciki.

Fitaccen mai shirya fina-finai a masana’anatar Kannywood Abubakar Bashir Mai Shadda ya lashe lambar yabo ta wanda ya fi yin fice a fageen shirya fim din harsunan cikin gida na MVCA Awards.

Bashir Mai Shadda ((Instagram/Bashir Mai Shadda)
Bashir Mai Shadda ((Instagram/Bashir Mai Shadda)

Mai Shadda ya lashe lambar yabon ce da fim din “Aisha” a rukunin fina-finan da ake shiryawa da harsunan cikin gida wanda Hausa na ciki.

“Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillaha, dukkanin godiya ta tabbata ga Allah Subhananu Wata’ala mai kowa mai komai, tsira da amince Allah su kara tabbata ga Fiyayen Halitta, Annabi Muhammad S.A.W.

Ali Nuhu a bikin MVCA (Instagram/Bashir Mai Shadda)
Ali Nuhu a bikin MVCA (Instagram/Bashir Mai Shadda)

“Ina mai sadaukar da wannan lambar yabo ga mahaifiyata, Hajiya Safiya Sani. Na gode Africa Magic.” Mai Shadda ya ce a lokacin da Rahma Sadau ta mika masa lambar yabon.

Bikin na Africa Magic Viewers Choice Award ya gudana ne a birnin Legas da ke kudu maso kudancin Najeriya a ranar Asabar.

T.Y. Sha'aban da Ali Nuhu (Instagram/Bashir Mai Shadda)
T.Y. Sha'aban da Ali Nuhu (Instagram/Bashir Mai Shadda)

Daga cikin fitattun ‘yan Kannywood da suka halarci bikin akwai jarumi Ali Nuhu da T.Y. Sha’aban.

Ga kadan daga cikin hotunan bikin:

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG