Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karamar Hukumar Kalabalge Na Neman Dauki


'Yan gudun hijira kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.
'Yan gudun hijira kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

Al'ummansu karamar hukumar Kalbalge a jihar Adamawa sama da dubu 40 suna bukatan taimako na gaggawa biyo bayan daidaita su da kungiyar Boko Haram tayi.

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kalabalge dake Jihar Borno Babagana Malarima ya jagoranci wata tawaga daga karamar Hukumar zuwa Abuja inda suka kawo kokon baransu zuwa wajen 'ya'yansu da ke majalisar kasa.

A wata hira da manema labarai bayan isarsu Abuja, Alhaji Malarima ya bayyana cewa mutanen al'ummaru sama da dubu 40 suna bukatan taimako na gaggawa saboda bisa ga cewarshi, abincin da mutanen da suke da shi gaba daya, Boko Haram sun hana su tabawa sun kore su baki daya daga garin. Yace zuwa gaba kadan, idan damina ta sauko, jama’a zasu shiga cikin yunuwa da matsala sosai saboda karancin abinci.

Kalabarge na daya daga cikin kananan hukumomin da kungiyar Boko Haram ta daidaita a jihar Borno, inda a halin yanzu dunbin al’ummar ke fakewa a dazuka dake kan iyaka tsakanin Borno da kasar Kamaru.

Ga cikakken rahoton da wakiliyarmu Sashen Hausa Madina Dauda ta aiko mana.

Rahoton Al'ummar Kalabalge - 2'05"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG