Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Tarwatsa Sansanonin 'Yan Boko Haram


Kakakin Sojojin Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade
Kakakin Sojojin Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade

A kokarin da suke yi na kakkabe 'yan Boko Haram sojoji sun sake tarwatsa wasu sansanonin kungiyar

Sojojin Najeriya sunce sun tarwatsa sansanin yan taadda har 10, kana sun kashe wasu da dama daga cikin su, duk kuwa wannan ci gaba ne da ganin sai sun kakkabe su gaba daya musammam daga dajin nan na Sanbisa inda nan ne matattaran su, a arewa maso mabashin Najeriya.

Mai Magana da yawun sojojin ta Najeriya Laftanar Kanar S.K Usman ya shaida wa wannan sashen cewa daya daga cikin sanannun sansanin nan na yan taaddan mai suna DURE na cikin wadanda aka tarwatsa a ranar asabar din nan data shige.

Sai dai yace Soja guda ya mutu, biyu kuma sun samu rauni sakamakon boma-boman da yan taaddansuka dasa a wasu wuraren nasu.

Usman yace har yanzu suna nan suna kokarin tantance adadin mutanen da suka samu rauni da kuma wadanda aka kubbutar, daga hannun yan boko haram din.

Nigeria da makwabtan ta da suka hada da Cameroun, Chadi,da Niger, sun kaddamar da fada ka in da na in domin ganin sun fatattaki yan kungiyar taboko haram,wanda ayyuukan su yayi dalilin lakume rayuka dubu 10 kana mutane sama da miliyan daya da rabi ne a yankin arewa maso gabashin Najeriya suka rasa matsugunnin su.

Tun a shekarar 2009 ne dai kungiyar boko haram take gasa wa yan yankin arewa maso gabashin Najeriya aya a hannu.

XS
SM
MD
LG