Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Mashako Na Ci gaba Da Yaduwa A Najeriya


Wani yaro ana yi mashi allurar rigakafi
Wani yaro ana yi mashi allurar rigakafi

Tun bayan da aka sa samu bullar cutar Mashako a watan Disambar 2022 a Najeriya, kasar ke bin hanyoyin dakile yaduwar ta, sai dai yanzu abin ya fara zama abin damuwa ga hukumomin lafiya.

A halin da ake ciki a yanzu ana fargabar mutum 11,587 sun kamu da cutar ta mashako yayin da aka tabbatar da mutane 7,202 a kananan hukumomi 105 daga jihohi 18 da ke fadin kasar sun kamu da cutar, inda cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 453 a Najeriya.

Kashi 73 cikin dari na wadanda suka kamu da cutar yara ne daga shekara 1 zuwa 14.

Jihar Kano na daga cikin jihohin da cutar ta fi kamari, sauran jihohin sun hada da Yobe, Katsina, Borno, Kaduna, Jigawa, Bauchi, Legas, FCT, Gombe, Osun, Sokoto, Niger, Cross River, Enugu, Imo, Nasarawa da jihar Zamfara.

Daraktan tsare-tsare bincike da kidiggiga na hukumar lafiya matakin farko a Abuja Dr Abdullahi Bulama Garba yace hukumar su da sauran masu ruwa da tsaki abangaren lafiya sun dauki dukkan matakan dakile yaduwar ta inda tuni aka fara bada rigakafin cutar a wasu jihohi.

A nasa bangaren Dr. Lawal Musa Tahir, na Asibitin Nizamiye a Abuja ya ce cutar mashako na farawa da mura da zazzabi ya kuma jaddada hatsarin cutar tare da bada shawara don daukar matakan kariya.

Hakan dai ya biyo bayan yaki da Najeriya keyi ne da cututtuka kamar zazzabin cizon sauro, Zazzabin Lassa, da kuma cholera.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG