Kungiyar kare hakkin dan adam ta IHRC-International Human Rights Commission ta shiga jerin masu bukatar majalisa ta sauya matsaya kan dakatar da Sanata Abdul Ningi.
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 20 ga watan Maris na kowacce shekara a matsayin ranar kula da lafiya da kuma tsaftar baki ta duniya.
Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta ce daga watan jiya na Febrairu, tashin farashin kayan masarufi a kasar ya kai 31.70%.
Mambobin kungiyar NUEE sun kasa sun tsare a gaban babban ofishin hukumar raba wutar lantarki ta jihar Kaduna.
A cewar masanin, lokaci ya yi da matasa za su kara mayar da hankalinsu kan koyon ilimin na'ura mai kwakwalwa wanda hakan zai ba su dama su yi aiki daga ko'ina a duniya.
Masana sun bayyana cewa, jan ragama da akalar rayuwar talakan kasa ya ta’allaka ne a wuyan gwamnati ta kowani fanni kama daga samar da ilimi, lafiya, tsaro da kuma abun dogaro da kai.
Ma’abota sauraron Sashen Hausa na Muryar Amurka na ci gaba da bayyana ra'ayoyin su kan cikar sashen shekaru 45 da fara aiki.
Sai dai a wannan shekarar, lamarin ya sha banban da yadda aka saba saboda farashin man fetur ya ninninka kudinsa: hakan ya haddasa tsadar kudin mota ninkin-ba-ninkin.
Wasu mata ‘yan jarida a arewacin Najeriya sun kaddamar da wani zaure da zai zama na hadin kai don karfafawa mata gwiwa domin yin aikin da samun nasarar gogaiya da sauran ‘yan jarida na kasa.
Shugaban Hukumar NAHCON Malam Jalal Ahmed Arabi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke bitar matakan da hukumar ke dauka don tunkarar aikin hajin da ke tafe na shekarar 2024.
Domin Kari