Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wata Hajiyar Da Akayi Tsammanin Ta Riga Mu Gidan Gaskiya A Turmutsutsun Saudiyya


Alhazai sun taru kusa da birnin Makka mai tsarki a Saudiya ranar Litinin 14 ga watan Oktoba shekarar 2013.
Alhazai sun taru kusa da birnin Makka mai tsarki a Saudiya ranar Litinin 14 ga watan Oktoba shekarar 2013.

An gano ‘daya daga cikin alhazan da suka bace, wadda ba’a sami jin labari ko gani ba sakamakon turmutsutsun da ya faru a lokacin aikin hajji a kasar Saudiya, hakan yasa bayan kammala aikin hajjin iyalan Hajiya Inno Issa, suka rugumi kaddarar cewa wata kila tayi shahada, kafin daga bisani aka ganota a wani asibitin kasar saudiyya.

Daya daga cikin ‘ya ‘yan Hajiya Inno, Mohammad Munnir yace sun kwashe kwanaki shida zuwa bakwai ana nemanta amma bawanda yasan inda take ba, to a rana ta bakwai sai aka sami labarin cewa akwai wani ‘dan jarida ya samu ‘daukar hoton ta ta wayar hannu, hakan ne yasa hankalinsu ya dan kwanta.

Wata babbar tawagar hukumar Alhazan Najeriya da ta hada da jami’ai da likitoci ne suka taryi Hajiya Inno a filin saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano.

Sannan aka wuce da ita zuwa gida inda gwamnan jihar Sokoto da tare wasu manyan jami’an gwamnati suka tarye ta.

Duk da yake har yanzu da alamar jinya ajikin Hajiya Inno, to amma akwai alamar ‘dan kwarin jiki a tare da ita.

‘yan uwa da abokan arziki dai sun nuna jin dadinsu da farin ciki. Daruruwan Mahajjata ne dai suka rasa rayukansu a wannan turmutsutsu na zuwa jifan Shedan a aikin hajjin da ya gabata a kasar Saudi Arabiya.

XS
SM
MD
LG