Tsohon dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Enugu ta Arewa kuma tsohon shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Ayogu Eze, ya rasu. Sanata Ayogu, ya rasu yana da shekaru 66 a duniya.
A ranar Asabar Rasha ta ce ta kama mutane 11 - ciki har da ‘yan bindiga hudu, kan harin da aka kai a wani zauren raye-raye na Moscow da kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa, yayin da adadin wadanda suka mutu ya kai 115.
Biyo bayan umurnin shugaba Tinubu na gaggauta ceto daliban Kuriga sama da 280, babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya ce sojoji sun dukufa wajen ganin an ceto daliban da kuma hukunta ‘yan bindigan da ke wannan aika-aika, da wasu rahotanni
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadan a Najeriya.
Jami'ai sun ce anga jinjirin wata a daren Lahadi a kasar Saudiyya, inda ake da wurare mafi tsarki a addinin Musulunci, wanda ke nuna yadda za a fara azumin watan Ramadan ga da yawa daga cikin musulmi biliyan 1.8 na duniya.
An yi ta harbe-harbe a babban birnin kasar Chadi a kusa da hedkwatar jam'iyyar adawa, bayan wata arangama da aka yi cikin dare a kusa da hukumar tsaron cikin gida ta kasar wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Hukumar zaben kasar Chadi ta ba da sanarwar ba zato a ranar Talata cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasa wanda zai kawo karshen mulkin soji na tsawon shekaru uku a yankin tsakiyar Afirka a ranar 6 ga watan Mayu.
Wani Sojin Saman Amurka ya mutu bayan da ya cinnawa kansa wuta a wajen ofishin jakadancin Isra'ila da ke Washington, D.C., yayin da ya bayyana cewa “ba zai kara kasancewa ba cikin masu kisan kare dangi.”
Matsin tattalin arziki a fadin Najeriya ya harzuka ‘yan kasa inda suka bazama kan tituna a wasu jihohi don nuna rashin jin dadinsu dangane da tashin gwauron zabin kayayyakin abinci da tsadar rayuwa a kasar.
Domin Kari