Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Karya Kumallo da Majalissar Wakilan Amurka


Jakadan Amurka Robert P. Jackson (File Photo)
Jakadan Amurka Robert P. Jackson (File Photo)

Jami’an gwamnatin Najeriya dana Amurka sunyi muhawara dangane da batun tsaro, musamman ma game da ceto daliban Chibok wadanda aka sace sama da kwanaki 87 kennan.

A taron karya kumalla da Majalisar Wakilan Amurka ta shirya jiya a fadarta dake nan Washington D.C, Jakadan Amurka Robert P. Jackson daga Ma’akatar harkokin wajen Amurka ya fara da bayyana dalilan barkewar rigingimun Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Game da batun daliban Chibok, Jakada Jackson yace “muna yin duk abinda zamu iya, amma a tunani na, akwai matukar muhimmanci in gaya muku cewa ko gwamnatin mu zata fuskanci kalubale, ita kadai tace zatayi kokarin ceto dalibai sama da 200. Muna gani yana da matukar muhimmanci a tattara bayanai da yawa, a yi shiri sosai, kuma gwamnatin Najeriya ta hada kai damu domin gani an ceto wadannan yara”.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG