Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeria Muhammad Buhari ya soma ziyarar nahiyar Turai yau


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Ziyarar ta shugaba Muhammad Buhari zata fara ne da kasar Faransa kafin ya wuce Ingila kasar da ta yiwa Najeriya mulkin mallaka

Da ya taso daga Abuja babban birnin Najeriya shugaban zai yada zango a birnin Strasbourg dake kasar Faransa.

Gobe Laraba uku ga watan Fabrairu shugaban zai yiwa majalisar tarayyar Turai jawabi na musamman inda duk 'yan majalisar zasu kasance tare da ministoci da manyan jami'an gwamnatocin kasashen Turai.

Ana kyautata zaton jawabin na shugaba Buhari zai fi mayar da hankali ne kan ta'adanci, matsanancin rikici da cin hanci da rashawa a Najeriya. Zai kuma tabo batun kalubalen tsaro a nahiyar Afirka da tattalin arziki da cigaba. Kana zai jaddada bukatar kasashen tarayyar Turai da wadanda suka cigaba su dada ba kasashen dake tasowa goyon baya.

Shugaba Buhari zai gana a kebe da shugaban majalisar tarayyar Turai Mr. Martin Schulz da kwamishanan majalisar Mr. Jean-Claude Juncker akan abubuwan da ya yi jawabi a kai kafin zuwa London inda zai shiga ayarin sauran shugabannin duniya a taron da aka lakabawa suna "Taimakawa Syria da Taron Koli". Dama an shirya a fara taron jibi Alhamis a birnin London hudu ga watan Fabrairun nan.

Shugaba Buhari zai yi anfani da zarafin da ya samu na kasancewa cikin taron da Birtaniya , Jamus, Norway, Kuwai da Majalisar Dinkin Duniya suka dauki nauyinsa ya kara jawo hankalin duniya da ta himmatu da halin da Najeriya ke ciki da wasu kasashen dake faman yaki da ta'adanci. Wajibi ne su goyi bayan kasashe irinsu Najeriya dangane da kokarin da su keyi na shawo kan illar ta'adanci da yadda ya shafi al'ummominsu.

Shugaban zai koma Najeriya a karshen mako.

XS
SM
MD
LG