Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pope Emeritus Benedict XVI Ya Rasu


Pope Emeritus Benedict XVI 
Pope Emeritus Benedict XVI 

Pope Emeritus Benedict na XVI (16), Fafaroma na farko da ya yi murabus cikin shekaru 600, ya rasu yana da shekara 95.

WASHINGTON, D.C - A wata sanarwar da mai magana da yawun fadar Vatican Matteo Bruni ya fitar a safiyar yau Asabar ta ce: “Cikin bakin ciki nake sanar da ku cewa Fafaroma Emeritus Benedict na 16 ya rasu a yau da karfe 9:34 a gidan ibada na Mater Ecclesia da ke fadar Vatican”.

Fafaroma Francis zai jagoranci jana’izar sa a dandalin St. Peter’s a ranar Alhamis, lamarin da ba a taba ganin irinsa ba inda wani Fafaroma dake kan mulki a yanzu zai yi bikin jana’izar tsohon.

-AP

XS
SM
MD
LG