Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Zata Buga Zargin da Take Yiwa Gwamnan a Jarida


Biyo bayan rashin samun nasarar mikawa gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura takardar argin da ake yi masa, majalisar tace zata buga zargin a jarida bisa ga doka

A cewar majalisar dokokin jihar Nasarawa gwamnan jihar Umaru Tanko Al- Makura ya gujewa karbar takardar da ta kunshi zargin da majalisar ke yi masa. Sabili da haka majalisar zata buga zargin goma sha shida a jarida kamar yadda doka ta tanada.

Jiya majalisar ta aikewa gwamanan takardar zargin da take yi masa. A takardar majalisar ta zargeshi da rashin gudanar da aikin jihar bisa doka da kin bin tsarin mulki. Lamarin na barazanar tsige gwamnan daga mukaminsa.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Mohammed Baba Ibako yace majalisar zata ba gwamnan kwana bakwai kacal daga ranar da suka buga zargin a jarida domin ya amsa. Tsarin mulki yace idan ba'a samu an ba gwamna takardar zargin ba hannu da hannu to sai a buga a jarida. Daga ranar da aka buga gwamnan yana da kwana bakwai ya bada ansa a rubuce. Sai a nada kwamiti idan kuma yaki bayyana a gaban kwamitin to duk abun da ya sameshi shi ya so.

Amma kwamishanan yada labarai na jihar Muhammed Hamza Elayo yace kawo yanzu basu samu takardar da 'yan majalisa suke ikirarin sun aikawa gwamnan ba. Batun wai gwamna ya kaucewa tsarin kashe kudin jihar, kwamishanan yace akwai ka'idodi da majalisa ta shimfida kuma bai ga inda gwamnan ya sabawa ka'idodin ba.

A wani mataki daban wasu matasan jihar sun fara bijirewa matakin da majalisar ta dauka. Wani Aliyu Ilele yace cikin shekaru goma sha biyu da suka gabata basu taba samun gwamnan da yayi aikin cigaban jihar ba kamar gwamnan yanzu. Dalili ke nan da matasan daga koina a cikin jihar suka taru a babban birnin jihar su nuna rashin amincewarsu da shirin tsige gwamnan.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG