Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Najeriya da Nijar Su Na Karatu Sosai a Makarantar Hadin Guiwa


Makarantar hadin guiwa tsakanin Jihar Kano a Najeriya da gwamnatin Nijar a Yamai, tana da dalibai 200 da suka fara karatu a harsunan Ingilishi da Faransanci

Watanni biyu a bayan da aka bude makarantar hadin guiwa wadda gwamnatin Jihar Kano a Najeriya tare da ofishin ministan ilmi na Jamhuriyar Nijar suka rattaba hannun ginawa a Yamai, yanzu haka an fara karatu ka'in da na'in tare da dalibai daga kasashen biyu.

Daliban da suka fito daga Najeriya a wannan makaranta sun tattauna da wakilinmu Abdoulaye Mamane Ahmadou cikin harshen Faransanchi da suka fara koya, har ma suka bayyana gamsuwarsu da yadda abubuwan suke gudana.

Wata tawaga karkashin jagorancin Kwamishinar Mata da Kyautata Halin rayuwar Al'umma ta jihar Kano, Dr. Binta Jibril, ta ziyarci wannan makaranta domin ganin irin ci gaban da aka samu, da halin da yaran makarantar suke ciki.

Kwamishinar ta ce abubuwan da ta gani, sun kayatar da ita, tana mai fadin cewa wannan makaranta zata kara dankon zumunci a tsakanin Najeriya da Nijar wadanda tun asali ma 'yan'uwan juna ne.

Ta ce ta yi farin cikin ganin yadda daliban makarantar suke zaune cikin farin ciki, suke kuma cudanya da junansu.

Ga rahoton da Abdoulaye Mamane Ahmadou ya aiko daga Nijar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG