Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SAUDIYA: Wata Kungiya ta Dauki Alhakin Kai Harin Garin Abha


Mataimakin Ministan Tsaron Saudiya Mohammad Al-Ayesh,
Mataimakin Ministan Tsaron Saudiya Mohammad Al-Ayesh,

Hijaz kungiyar da ba'a taba jin sunata ba mai alaka da kungiyar ISIS ta fito fili ta dauki dauki alhajin kai hari a masallacin jami'an tsaro dake garin Abha

Wata kungiya dake da nasaba da kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin da aka kai jiya wanda yayi musabbabin kashe mutane 15 a masallacin dake kasar Saudiyya wanda mafi ya yawan masu anfani da wannan masasllacin jamiaan tsaro ne.

Kungiyar wadda ta kira kanta Hijaz tace ba shakka ita ce ta aikata wannan aika-aikan.

Kungiyar dai tana bayani ne a cikin shafinta na sakon Twitter awoyi bayan da wani dan kunar bakin wake ya fasa bom din da yake dauke dashi a wani masallacin dake kudancin birnin Abha.

Birnin na Abha dai yana kusa dabakin iyakar kasar Saudi Arabia ta kudancin bakin iyaka da Yemen wadda yaki ya dai-daita.

Sai dai kwamitin tsaro ta MDD a wani sanarwan da ta bayar tayi ALLAH waddarai da wannan harin, kuma tace wajibi a mike tsaye domi ganin an ga bayan kungiyar ta isis.

XS
SM
MD
LG