Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Bukaci Mutane Su Sauya Salon Kula Da Lafiyarsu


Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani

Wasu daga cikin likitocin da suka kware a wannan fanni sun ce rashin fahimtar tasirin motsa jiki don kula da gabbai, yana matukar nakasa rayuwar mutane da dama a Najeriya.

Ganin yadda mutane da dama kan ci abin da suka ga dama kuma su ki kulawa da lafiyarsu, ya sa gwamnatin Jihar Kaduna ta nuna bukatar maida hankali wajen motsa jiki da kuma neman likitocin kashi don neman waraka ba tare da shan magani ba.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe wadda da ma likita ce, ta ce motsa jiki kadai zai iya magance cututtuka da dama ba tare da shan magani ba.

Mataimakiyar gwamnan, wadda kwamishiniyar lafiya, Dr. Umma Ahmed ta wakilta wajen taron ranar likitocin kashi da motsa jiki ta duniya da ya gudana a jami'ar jihar Kaduna, ta ce likitocin kashi za su sami dukkan goyon baya daga gwamnatin Jihar Kaduna.

Taken taron likitocin kashi da motsa jiki na bana dai shi ne, hanyoyin magance cututtuka ba tare da shan magani ba.

Shugaban kungiyar likitocin kashi da motsa jiki wadanda ba sa amfani da magani wajen magance cututtuka na jihar Kaduna, Dr. Bashir Sabo ya ce da yawan mutane ba su fahimci aikinsu ba.

Karancin likitocin kashi da motsa jiki dai na cikin manyan matsalolin da taron na bana ya tattauna.

Sai dai mataimakin shugaban jami'ar jihar ta Kaduna, KASU Prof. Abdullahi Musa ya ce, jami'ar na shirin magance wannan matsala ta hanyar ware kudi don kula da tsangayar karatun likitocin wannan fanni.

Wasu daga cikin likitocin da suka kware a wannan fanni sun ce rashin fahimtar tasirin motsa jiki don kula da gabbai na matukar nakasa rayuwar mutane a Najeriya.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG