Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dakatar Da Jarumi Abdul Sahir Daga Shiga Fina-finan Kannywood


Abdul Saheer
Abdul Saheer

Na wallafa bidiyon ne don jan hankalin mata masu rawa a TikTok da damummun kaya domin su daina abin da suke yi - Sahir

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta sanar da dakatar da jarumi Abdul Sahir, wanda aka fi sani da ‘Malam Ali’ daga fitowa a duk wani fim ko wata harka da ta shafi Kannywood har tsawon shekaru biyu.

Shugaban hukumar, Abba Almustapha ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wata hira da ya yi da manema labarai.

“Hukuma ta yanke hukuncin cewa ta dakatar da Abdul Sahir jarumi, wanda ake wa lakabi da Malam Ali daga fitowa ko kuma mu’amala ko kuma duk wani abu da ya sani na harkar fina-finai na Kannywood har na tsawon shekara biyu.” In ji Almustapha.

Kannywood, wacce hedkwatarta ke birnin Kano a arewa maso yammacin Najeriya, ita ce masana'antar shirya fina-finan Hausa a Najeriya.

Shugaban hukumar ya kara da cewa dalilin dakatar da jarumin shi ne sakin wani bidiyo da ya saba ka’idar hukumar.

“Wannan bidiyo da ya sake, bidiyo ne na batsa da cin mutunci da cin zarafi ga al’umar Musulmi baki daya, wanda wannan hukuma ba za ta taba yarda da wannan ba.”

Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba Almustapha
Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba Almustapha

Almustapha ya kara da cewa daukan wannan mataki ya biyo bayan korafe-korafe daga kungiyoyin na fim, kamar na jarumai, da malamai da kuma daidaikun mutane da ke cikin jihar Kano.

Shugaban hukumar ya kara da cewa, sun gayyaci jarumin domin ya zo ya kare kansa, amma ya ki amsa gayyatar.

“Mun gayyace shi, mun ba shi lokaci yau (Litinin) karfe 10 na safe domin ya zo ya amsa tuhume-tuhume, kuma ya kare kansa, wanda har yanzu da nake muku magana karfe 5 da wani abu bai zo ba, ba mu ji daga gare shi ba, bai yi waya ba kuma bai turo ba.

“Wannan shi ya kara tabbatar mana da cewar ya yi ne domin ya ci zarafin al’umar jihar Kano da kuma Musulunci baki daya.” In ji Al Mustapha.

A wata hira da ya yi da Muryar Amurka, Almustapha ya ce sun kai batun gaban kotu “don ya girbi abin da ya shuka.”

Ya kara da cewa, Malam Ali (Sahir) ya ba su tabbacin cewa zai amsa gayyatarsu da misalin karfe 10 na safen ranar Litinin, amma kuma bai je ba.

Sahir, ya yi fice ne bayan da ya fara fitowa a shirin Kwana Casa'in na Arewa 24 a 'yan shekarun baya, inda ake mai lakabi da Malam Ali.

Shirin Kwana Casa'in (Hoto: Facebook/Arewa 24)
Shirin Kwana Casa'in (Hoto: Facebook/Arewa 24)

Yayin da yake mayar da martani, Sahir ya ce dalilin da hukumar ta bayar na dakatar da shi bai kai a dauki wannan mataki ba.

“Bidiyon da na yi, na fadakarwa ne akan mata da suke sa damammun kaya, suna zubar da mutuncin kansu suna rawa, suna gantsare-gantsare a TikTok.” In ji Sahir.

A cewarsa, ya yi amfani ne da wani salo a matsayinsa na jarumi wajen aikawa da sako don fargar da mata daga fadawa tarkon maza masu yaudara, wadanda suke musu alkawarin za su aure su amma kuma su gudu bayan sun samu abin da suke so.

“Abin da yake faruwa kenan a ‘society’ dinmu (al’umarmu) namiji zai zo ya yaudari yarinya da cewa zai aure ta, ya yi abin da zai da ita daga baya ya zo ya gudu ya bar ta.

“Ya kamata a ce sai ta wannan hanyar ya kamata na turawa mutane wannan sako su fahimta, sai na yi amfani da wannan hanyar na yi posting, sai aka je ana yanka bidiyon nawa.”

Ya kara da cewa, ya rubuta sakon gargadi a kasan wannan bidiyo da ya wallafa inda ya ce, “wannan bidiyon na yi shi ne saboda wa’azantarwa da fadakarwa, yana nan ban goge ba.”

Dangane da gayyatar da aka yi masa ya ki amsawa, Sahir ya ce lallai ya fadawa hukumar cewa zai je amma rashin lafiya ya kada shi.

Bana Bakwai, wani fim din masana'antar Kannywood
Bana Bakwai, wani fim din masana'antar Kannywood

“A jiya Lahadi, ina komawa gida, sai Allah ya jarrabe ni da rashin lafiya, da ma na dan yi rashin lafiya kwanaki, aka dauke ni ranga-ranga aka kai ni asibiti, a asibitin na kwana.

“Da na san ba zan samu zuwa wannan 'meeting' din ba, shi wanda ya kira ni ya ce ana gayyata ta, sai da na kira shi sau biyar bai dauka ba.”

“Sai bayan da na ga wannan sanarwar (ta dakatarwa) sai na kira shi, kuma ya dauka, sai ya ce min na yi hakuri ya ga ‘missed calls’ dina amma bai dauka ba. Wai sai ya ce min shi bai ma kalli bidiyon da ya sa aka yanke min wannan hukuncin ba.

Sahir ya kara da cewa, bayan dakatar da shi, ya kira Almustapha sau hudu amma bai dauka ba sannan ya tura mai sakon tes da WhatsApp bai amsa ba.

“Yanzu kuma ban san mataki na gaba da zan dauka ba, domin an ce an riga an dakatar da ni.” Sahir ya ce.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake dakatar da jarumi a masana'antar ta Kannywood ba, a shekarar 2016 da 2020 an taba dakatar da jaruma Rahama Sadau bisa wasu laifuka da aka yi zargin sun saba ka'idar masana'antar.

Saurari hirar Baraka Bashir da Abba Almustapha da kuma Abdul Sahir:

An Dakatar Da Jarumi Abdul Sahir Daga Shiga Fina-finan Kannywood - 8'52"
please wait

No media source currently available

0:00 0:08:52 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG