A yau, ranar da ake kira 'Good Friday', wato Jumma'a mai kyau, rana ce da mabiya addinin Kirista ke imanin an giciye Yesu Kristi, kamar yadda Allah ya tsara, domin ya kasance mai ceton dukkan bil'adam, daga shiga jahannama.
Kasa da sa’a 24 bayan fitar da sanarwar da hedkwatar tsaron Najeriya ta yi, basaraken, Clement Ikolo ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar Delta inda ya ce ba shi da hannu a kisan sojojin.
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna yayi tayin bada ilmi kyauta ga daliban makarantar Kuriga da aka kubutar a karkashin gidauniyarsa.
A ranar Alhamis ne Shelkwatar Tsaron Najeriya ta bayyana cewar, Babbar Kotun Tarayya dake Borno ta bada umarnin sakin akalla mutane 313 da sojoji suka kana a bisa zarginsu da aikata laifin ta'addanci.
A daidai lokacin da wasu ‘yan Najeriya ke korafe-korafe a kan kayyade yawan kudin da zasu rika cira a ATM ko kuma a cikin banki da ake kallo a matsayin yiwuwa akwai karancin takardun kudi ne a kasar, masu ruwa da tsaki a fannin hada-hadar kudi a bankuna sun ce babu matsalar karancin kudi.
Shugaban kamfanin Binance dake tsare a hannun hukumomin Najeriya, Tigran Gambaryan ya maka Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu da Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a kotu bisa zarginsu da tauye masa hakkokinsa na bil adama.
Tun dai bayan dawowar daliban Kuriga da na jihar Sakkwato da ‘yan bindiga suka sace domin karbar kudin fansa, ake ta samun ra'ayoyi mabambanta dangane da yadda aka ceto daliban.
Najeriya za ta ba da sabbin lasisin hakar ma'adinai ne kawai ga kamfanonin da suka gabatar da wani shiri kan yadda za a sarrafa ma'adanai a cikin gida, karkashin sabbin ka'idoji da ake samar da su, kamar yadda kakakin gwamnati ya tabbatar a ranar Alhamis.
Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana wasu mutane 8 da ake nema ruwa a jallo kan kashe jami’an soji a yankin Okuama da ke jihar Delta.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karama zaratan dakarun Rundunar Sojojin Najeriya da wadansu batagari dake kauyen bakin teku suka yiwa kisan gilla da lambar girmamawa na kasa.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya gana da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a fadar aso Villa dake birnin Abuja inda suka tattauna karuwar hare-haren ‘yan bindiga da wasu nau’ukan ta’adanci a jiharsa.
Masana tsaro da sauran jama'a a Najeriya na ci gaba da tsokaci tare da nuna jin dadi, a kan labarin mutuwar kasurgumin ‘dan bindigan nan Dogo Gide da aka tabbatar da mutuwar sa a jihar Sokoto.
Domin Kari
No media source currently available