Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijira Daga Damboa Sun Isa Gombe


Gidajen da motoci da aka kone
Gidajen da motoci da aka kone

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Gombe ta samu 'yan gudun hijira da dama daga Damboa jihar Borno wadanda suke gujewa hare-haren da 'yanbindiga ke kai masu ba kama hannun yaro

Cikin kwanaki uku hukumar tayi rajistan mutane fiye da dubu daya daga karamar hukumar Damboa dake cikin jihar Borno.

Shugaban hukumar Dr Danlami Arab Shukudi ya bayyanawa wakiliyar Muryar Amurka cewa cikin kwana uku da suka gabata hukumarsa ta samu fiye da mutane dubu daya kuma har yanzu suna kara isowa garin Gomben. Yadda mutanen ke kwararowa ya fi karfin duk tunanensu a hukumance.

Can tashar Dadinkowa inda motoci ke saukar da mutanen an ga wasu da yawa kara zube. Dr Shukudi tace sai sun tantance mutanen kafin su yi masu rajista. Bayan sun tantance idan an samu gida sai a basu ko kuma kayan tallafi kamar kayan kwanciya da makamantansu da kayan abinci.

Domin a tabbatar cewa bata gari basu shiga lamarin ba akan kai kayan agajin ne wurin masu anguwanni su raba domin su suka san mutanen anguwansu da wadanda suke gudun hijira.

Mutanen Damboan da suka gudu sun ce fada ne ya korosu domin babu wurin da zasu sa kai. Sun sha wahala akan hanya kafin su iso Gombe.

Ga rahoton Sa'adatu Fawu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG