Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wannan Gidauniya Maganar Banza Ce Da Rainin Wayo Inji Hajiya Hafsat Marshal


Hajiya Hafsat Ahmed Marshal marubuciya, 'yar gwagwarmaya kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum
Hajiya Hafsat Ahmed Marshal marubuciya, 'yar gwagwarmaya kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum

Hajiya Hafsat ta ce a Najeriya duk wata haraka ta zama ta karya, ta almubazzaranci, ta cuta

Ranar Alhamis shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya shirya kuma ya jagoranci kaddamar da gidauniyar taimakon wadanda bala'in ta'addancin Boko Haram ya rutsa da su.

A yayin kaddamar da gidauniyar an tara kudade kusan Naira Miliyan Dubu Sittin.

A kan wannan shiri na kaddamar da gidauniyar tallafawa wadanda ta'addanci ya kassara a Najeriya, Grace Alheri Abdu ta tattauna da Hajiya Hafsat Ahmed Marshal, marubuciya, 'yar gwagwarmaya kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, wadda ta furta albarkacin bakin ta kamar haka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

Daidaikun mutane da kungiyoyi ne su ka bayar da gudunmowa baicin gwamnatin tarayyar Najeriya da ta zubawa gidauniyar Naira miliyan dubu 10.

Ana kyautata cewa za a yi amfani da kudaden wajen sake tsugunar da wadanda bala'in ta'addanci ya tarwatsa a duk fadin kasar Najeriya tare da farfado mu su da hanyoyin yin rayuwar su ta yau da kullum.

Mutane fiye da dubu goma sha uku ne suka hallaka cikin hare-haren 'yan Boko Haram a yayin da wasu dubban daruruwa suka bar wuraren su, kuma dubban kadarori da dukiyoyin jama'a suka salwanta.

XS
SM
MD
LG