Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kafa Jami’ar Tsaro Da Hadin Gwiwar Jami’ar Abuja


Maj. Hamza Al-Mustapha a wani hoto da aka dauka a 2012.
Maj. Hamza Al-Mustapha a wani hoto da aka dauka a 2012.

A yayin da masu hannu da shuni suka dimauce cikin hadama wajen rashin ganin mutuncin kowa sai kudi, kazalika suka dauka adalcin doka bai kamaci dukkan Dan Adam ba. hakkan zai bada dama wajen bullar ta’addanci da hakan zai yi wuyar shawo kai sai an sha wahala.

Manjo Hamza Al-Mustapha yayi magana wajen taron sanya hannu a yarjejeniyar kafa jami’ar tsaro da hadin gwiwar jami’ar Abuja, saboda koyon dabarun kaudabara daga ‘yan ta’adda musammam ma ‘yan Boko Haram.

Al-Mustapha wanda yake tsohon jami’in tsaro ne da yayi aiki da Janal Sani Abacha, yace wannan nau’in jami’ar tsaro zata zama ta farko a Najeriya da ma nahiyar Afirka.

Manjo Al-Mustapha ya tallafawa jami’ar Abuja da wasu motocin safa don jigilar ‘dalibai, da hakan zai share fagen fara aikin wannan jami’ar, da samo kwararru daga gamayyar cibiyoyin asiri na tsaron Najeriya.

In za a tuna dai tsohon shugaba Jonathan yace da makaman da yayi oda ne ake amfani wajen yaki da Boko Haram, yana mai cewa a shirye yake ya tallafawa gwamnatin Buhari a duk inda ya dace ko kuwa ake ganin zai iya bada gudunmawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG