Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya ta Zamo Shugabar Hukumar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shugabancin hukumar tsaro na majalisar dinkin duniya na karba karba kowane wata ya fada kan Najeriya a wannan watan Augusta.

Najeriya ta karbi shugabancin hukumar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya wannan watan.

Jakadiyar Najeriya ta din-din din a majalisar Prof. Joy Ogwu ta karbi ragamar shugabancin daga hannun Jakada Gerard van Bohemen mai wakiltar kasar New Zealand wanda ya shugabanci hukumar a watan Yulin shekarar 2015.

Mai magana da yawun jakadiyar Najeriya Dr Tope Adeleye Elias-Fatile yace wannan ne karon farko a tarihin Majalisar Dinkin Duniya da wata kasa da aka zaba zata jagoranci hukumar sau hudu a wa'adi biyu cikin shekaru biyar. Ya bayyana cewa an zabi Najeriya ta kasance cikin hukumar amma ba mai kujerar din-din-din ba ranar 17 ga watan Oktobar 2013 kuma yanzu tana karo na biyu na shekarar 2014 zuwa 2015.

Dr Tope yace wannan shi ne karo na biyar tun lokacin da Najeriya ta samu 'yancin kai da ake zabar Najeriya ta zauna cikin wannan hukuma ta Majalisar Dinkin Duniya mai ikon gaske. Ita hukumar tana da alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duk fadin duniya. Da can Najeriya ta kasance cikin hukumar a shekarun 1966 zuwa 1967 da 1978 zuwa 1979 da 1994 zuwa 1995 da kuma 2011 zuwa 2012.

A watan Janairun 2014 aka sake zabar Najeriya ta kasance a hukumar bayan ta bar hukumar a watan Disamban 2012. Wannan shi ne lokaci ma fi karanci da wata kasa zata gama wa'adi a kuma sake zabarta ta cigaba ta kuma karbi shugabanci a tarihin Majalisar Dinkin Duniya.

XS
SM
MD
LG