Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai ta Amince Kananan Hukumomi Suci Gashin Kansu


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

An dadae ana batun 'yancin kananan hukumomin Najeriya. A wata fira da abokin aiki yayi da wakiliyar Muryar Amurka majalisar wakilai ta amince da bukatar to amma akwai jan aiki a gaba kafin amincewar ta zama doka.

Majalisun kasar Najeriya suna kokarin yiwa kundun tsarin mulkin kasar gyaran fuska.

An dade ana kokarin gyaran kundun tsarin mulkin. A majalisun baya an yi irin wannan yunkurin. An so a yi gyara akan baiwa kananan hukumomi damar cin gashin kansu.

A wannan karon maganar 'yancin kananan hukumomi ta sake kunno kai. Majalisar waikilai ta amince da haka. Majalisar dattawa ita ma ta amince da baiwa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu amma bata amince da batun cirewa shugaban kasa da gwamnoni kariya ba, maganar dake hade da na kananan hukumomi. Wannan ya nuna akwai rashin jituwa tsakanin majalisun biyu.

Idan har majalisun basu yadda akan kowace irin magana ba zata yiwu ba a mika maganar ga majalisun jihohi. Domin dole sai da amincewar majalisun jihohi za'a iya yiwa kundun tsarin mulki gyaran fuska ta kuma zama dokar kasa.

Akan ko za'a iya yin gyaran kafin a yi zaben shekara mai zuwa wakiliyarmu tace zai yi wuya a samu dokar ta tabbata kafin zaben. Babu yadda dokokin zasu kai jihohi a yi muhawara akansu kana su zama doka cikin watanni uku da suka saura kafin a yi zabe.

To saidai bayan zabe za'a cigaba da maganar a sabbin majalisun dake zuwa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG