Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiran Sarkin Kano Nada Goyon Baya


Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na Biyu yana ziyartar wadanda harin bom din Makaratar Malaman Tsafta na Kano ya shafa, a asibitin Murtala dake Kano. Yuni 24, 2014. (File Photo)
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na Biyu yana ziyartar wadanda harin bom din Makaratar Malaman Tsafta na Kano ya shafa, a asibitin Murtala dake Kano. Yuni 24, 2014. (File Photo)

Kiran da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi na biyu yayi, na cewa al-umma su tashi, su kare kawunansu, yana samun goyon bayan jama’a.

Biyo bayan kwace jihohin Mubi da Maiha dake Jihar Adamawa, da ‘yan kato da gora suka yi daga hannun mayakan Boko Haram, lamarin da ya kara wa jama’a kwarin gwiwa game da kokarin kare kawunansu.

Al ummar Kaduna da kewaye, sun tofa albarkacin bakinsu game da furucin da Sarkin Kano yayi.

“Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi, Allah Ya kara mishi daukaka, yayi mana tuni akan abunda yi. Wajibi ne muna tsaron garuruwanmu, da kauyakunmu, da gonakinmu. Domin tsaro bana mutum daya bane. Tsaro na kowa ne, tunda jami’an tsaron nan basa iya tsare rayukanmu da dukiyoyinmu, wajibi ne mu kare kanmu,” a cewar wani mazaunin birnin Kaduna.

Wata mace cewa tayi “ina goyon bayan maganar Sarkin Kano, na cewa talakawa su fito su kare kansu. Ya kamata talakawa mu fito mu kare kanmu da kanmu.”

Mafi yawancin jama’ar da Sashen Hausa na Muryar Amurka yayi magana da su na goyon bayan tanadin da zai shirya jama’a su kare kawunansu, saboda gazawar jami’an tsaron Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG