Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Conseil De’ L’entente Zasu Yaki Ta'addanci


Wani soja mayakin sama kusa da sansanin sojoji dake Niamey in Niger.
Wani soja mayakin sama kusa da sansanin sojoji dake Niamey in Niger.

Kasashen kungiyar Conseil De’ L’entente zasu hada hannu wajen yaji da ayyukan ta'addanci da kuma shawo kan matsalolin da kasashen ke fuskanta,

Ministocin kungiyar kasashen CONSEIL DE L'ENTENTE da suka hada da Nijer,Cote d'ivoire,Burkina fasso,Benin,da Togo na halarta wani taron kolin kasashen domin duba matsalolin da kasashen minbobin kungiyar ke fuskanta.

Taron na wuni daya da ministocin kasashen Conseil De’ L’entente ke halarta a birnin Niamey zai tattauna ne a kan matsolin da kasashe biyar membobin kungiyar ke fuskanta da suka hada da matsalolin tsaro da kiwon lafiya da bunkasar tattalin arziki.

Taron zai kuma tattauna a kan sauran matsaloli da kasahen kungiyar ke fuskanta.

Taron dai yazo ne a daidai lokacin da kasashen ke fuskantar wadansu matsalolin tsaro da suka shafi ayyukan ta’addanci.

Daga Niamey Abdoulaye Mamane Amadou ya aiko mana da wannan rahoton

Taron kasashen Conseil De’ L’entente :3:30
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG