Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janaral Babangida Yayi Allawadai da Harin da Aka Kai Kan Janaral Buhari


Janar Muhammadu Buhari Mai ritaya
Janar Muhammadu Buhari Mai ritaya

Tsohon shugaban kasar Najeriya Janaral Ibrahim Babangida ko IBB yayi allawadai da harin da aka kaiwa tsohon shugaban kasar Janaral Muhammed Buhari da kuma Shaikh Dahiru Bauchi a garin Kaduna.

Janaral Babangida yace lamarin abun takaici ne saboda haka ya bayyana bukatar ganin 'yan Najeriya sun hada kai domin kawar da bala'in da ya addabi arewacin kasar.

Tun farko Janaral Babangida ya fara yin jaje ne ga wadanda lamarin ya rutsa dasu ko suka jikata. Yace duk wani dan Najeriya ba zai ji dadin hakan ya faru ga kowa ba. Ya kira gwamnati da a cigaba da kula da sha'anin tsaro a kasar. A dinga sa ido akan abubuwa dake faruwa yanzu.

Dangane da tunanensa yace abu ne ya faru kuma yana faruwa tilas ne jama'ar kasar da gwamnati a hada karfi da karfe a samo hanyar da za'a gyara wannan matsala da ta addabi kasar.

Gwamnoni goma sha tara na arewacin kasar sun fitar da wata sanarwa ta yin allawadai da abun da ya faru. Shugaban gwamnonin gwamna Babangida Aliyu na jihar Neja yace lamarin ma ya daure masu kai. Sakataren gwamnatin jihar Neja Alhaji Idris Ndako shi yayi bayani a madadin gwamna Babangida Aliyu. Yace gwamnonin arewa basu ji dadain abun da ya faru ba. Suna rokon gwamnatin tarayya ta kara kokari.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG