Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: INEC Na Daurar Dammarar Hana Magudi


Na'urar Karanta PVC
Na'urar Karanta PVC

A wani bangare na kawo sauye-sauye kan yadda ake zabe a Najeriya hukumar zaben ko INEC ta bullo da tsarin yin anfani da naurar tantance masu zabe.

Naurar da take kamar waya tana tantance duk wanda ya zo kada kuri'a. Duk abun dake cikin katin mutum nauarar zata nuna. Zata nuna suna da garin mutum da dai sauransu. Kuma duk wanda yazo da katin da ba nashi ba naurar ba zata yi aiki ba.

Hukumar tace ta shirya za'a fara aikin tantancewar ne daga karfe takwas na safe zuwa karfe daya na rana a ranar zaben. Daga bisani kuma za'a ba masu zabe dama su jefa kuri'a.

'Yan siyasa a Kano na bayyana ra'ayoyi daban daban akan sabon tsarin. Alhaji Rabiu Abdullahi Garindanga wani jigon jama'iyyar APC a Kano yace tara mutane wuri guda daga karfe takwas zuwa karfe daya kafin a soma jefa kuri'a nada matsala. Yakamata a sake. Kamata yayi da an tantance mutum a barshi ya jefa kuri'a kana ya kama gaban kansa.

Kwamred Muhi Magaji mutumin da ya nemi APC ta tsayar dashi dan takarar kujerarar majalisar wakilan Najeriya yace a ganinsa babu wata matsala da sabon tsarin da hukumar ta fito dashi. Shirin alamar cigaba ne.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

XS
SM
MD
LG