Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hafsan Sojojin Najeriya Ya Dakatar da Hukuncin da Aka Yiwa Wasu Sojoji


Janar Yusuf Tukur Burutai hafsan sojojin Najeriya
Janar Yusuf Tukur Burutai hafsan sojojin Najeriya

A lokacin Janar Minimah hafsan sojojin Najeriya a karkashin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan aka zargi wasu sojoji da laifuka har aka yiwa wasu hukuncin dauri ko kisa.

Bisa ga korafe-korafen da aka dinga yi akan hukuncin da aka yiwa wasu sojojin Najeriya da karar da su sojojin suka kai hukumar sojin suka sa Janar Burutai sabon hafsan sojojin ya bada umurnin dakatar da duk hukuncin da aka yi.

Kanal S.K.Usman mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya ya bayyana dalilan da suka sa Janar Burutai ya dakatar da duk wani hukuncin da aka yi ko kuma ake shirin yi akan sojojin. Yace suna ganin ba'a yi masu adalci ba saboda haka za'a gudanar da bincike a tabbara an yi adalci.

Wani hafsan soji mai murabus Aliko El-Rashid ya yi maraba da umurnin. Yace duk inda aka samu tawaye kamar Dimokradiyar Kwango na M23 da na Iraqi da na Kudancin Sudan duk sojoji ne da suka balle sabo da rashin gaskiya da aminci. Saboda haka abun da Janar Burutai yayi ya yi daidai. Yace a duba wadanda basu yi laifi ba a dawo dasu.

To amma masu sharhi akan tsaro a Najeriya na ganin umurnin hafsan sojojin ba zai rasa nasaba da karancin sojoji ba. To amma Kanal S.K.Usman ya dage korafe korafe ne suka sa domin shugaban sojojin na yanzu yana da hazaka da son aiwatar da gaskiya da hangen nesa. Saboda haka idana aka kawo koke a tabbatar an yi da'a an yi shari'a tsakani da Allah..

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG