Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari ZA ta Biya Kudin Tallafin Man Fetur


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Shugaba Buhari ya mikawa majalisun kasar karamin kasafin kudi da zummar biyan kudin tallafin man fetur domin a kawo karshen dogayen layuka a gidajen man kasar saboda karanci.

Gwamnatin Buhari zata biya kudin tallafin man fetur da ya dara nera biliyan dari hudu.

Karancin man fetur ya sa masu sayar dashi a kasuwar bayan fage suna cin karensu ba babbaka.

Babbar sakatariyar ma'aikatar man fetur Dr Jamila Shuara tana ganin gina rumfunan adana man fetur ya dace gwamnati ta yi saboda gujewa sake samun karancin man nan gaba.

Dan kasuwar man fetur Awal Awaliya na ganin cire tallafin man fetur din gaba daya shi ne kawai mafita domin zai sa 'yan kasuwa kawo man ba tare da jiran kudi daga gwamnati ba.. Yace kowane dan kasuwa zai je ya sayo mai ya sayar yadda ya saya. Wannan zai kawar da dogon layi. Ya kira mutane su tuna biyan kudin tallafi wa dilallan man fetur ba kyauta ba ne. Kudinsu ake mayar masu.

Yanzu dai majalisar dattawa tace zata yi hanzarin amincewa da bukatar ta shugaban kasa domin biyan kudin tallafin. Sanata Danjuma Goje shi ne shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa. Yace zasu tabbatar sun ba shugaban kasa abun da ya bukata. Nan da zuwa Talata zasu mikawa shugaban amincewarsu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG