Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shirya Wa Mata Lacca A Kano Albarkacin Ramadan


Wasu mata a taron addini
Wasu mata a taron addini

Wata kungiyar addinin Musulunci, SISAP a takaice, ta shirya wa mata lacca don karuwa a addinace da kuma zamantakewar yau da kullum.

Wata gidauniyar tallafa wa mata musamman ma na karkara, SISAP a takaice, ta shirya ma mata lacca mai taken Nasihohi Ga Mata. Abin da gidauniyar ta sa gaba sun hada da kiwon lafiya da ilimi da kuma taimaka ma marayu da sauransu.

Hajiya Tasidi Zakari Garin Babba, daya daga cikin shugabannin gidauniyar ta ce babban burinsu wannan karon shi ne su jawo hankalin mata kan wasu matsaloli kuma suna da kwararru a fannoni dabandaban da kan taimaka. Ta ce kodayake laccar ta fi ta’allaka kan addini, an kuma tabo batun kiwon lafiya kuma likitocin da ke wurin sun warare matsalolin.

Limamin Masallacin Alfurkhan da ke Kano, Dakta Bashir Aliyu Umar, wanda ya gabatar da babbar laccar y ace an yi magana kan Ruhin Azumi, da hukunce hukuncen da su ka shafi mata a watan azumi – musamman game da niyya da kuma uzuri. Na ukun, in ji shi, shi ne abubuwan da ke a matsayin zayyana, wadanda ke cika da azumi da yawaita kyauta ga mabukata da yawan istigifari da dai sauransu. Matan sun bayyana gamsuwa da kuma amfana da laccar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG