Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Jami'an Tsaro Hudu a Yemen


Baraguzan motar da aka kaiwa hari.
Baraguzan motar da aka kaiwa hari.

Mahukuntan kasar Yemen sun tabbatar cewa 'yan ta'ada masu alaka da kungiyar al-Qaida sun kashe jami'an tsarota guda hudu

A Yemen jami’an kasar sun ce an kashe jami’an tsaro hudu a wani jerin hare hare da ake aza laifin kan mayakan sakai cikin kwanaki biyu da suka wuce.

Ana zargin wasu mahara kan babura ne suka kashe uku daga cikin jami’an tsaron a San’a babban birnin kasar.

Hare haren sun biyo bayan farmaki da aka kai da jiragen yaki da suka yi sanadiyyar mutuwar mayakan sakai ‘yan al-Qaida su 55 a kudancin kasar. Ana kyautata zaton Amurka ce ta kai hare haren da jiragen yakin nan da basu da matuka.

Kungiyar al-Qaida a Yemen ta kaddamar da hare hare kan kan cibiyoyin soja, da ‘yan yawon bude ido, da jami’an difilomasiyya cikin ‘yan shekarun nan da suka wuce.

A cikin makon jiya reshen kungiyar ta al-Qaida a Yemen, tayi alwashin zata kai karin hare hare kan abunda ta kira “muradun kasashen yammacin duniya”.
XS
SM
MD
LG