Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amfani Da Matasa Wajen Kawo Tsaro Da Ci Gaban Al’ummar Adamawa


A wani sabon yunkuri na magance matsalar tsaro a tsakanin al’umma ,yanzu haka manyan masarautun jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya sun kaddamar da wani sabon shiri na amfani da matasa domin tabbatar da zaman lafiya.

Manufar shirin shine zaburar da matasa domin zama jakadu nagari inda suke kafa kungiyoyin sintiri dake tallafawa jami’an tsaro. Matasa dai sun yunkuro domin kare rayukan mutane da dukiyoyin al’ummar Adamawa.

Tun farko dai mai martaba Alhaji Umaru Adamu Sanda ya bayyana muhimmamcin tafiya da matasa, inda yace akwai sarakunan matasa na masarauta da kuma na gundimomin hakimai, ana kuma kula da ayyukan da yakamata suyi, kamar na tabbatar da zaman lafiya da hana su shaye shaye da hana amfani da matasa wajen fadace fadace na siyasa.

Baya ga sintirin sa kai sarakunan matasa kan taka muhimmiyar rawa wajen magance rikici a cikin al’umma musammmam na makiyaya da manona.

XS
SM
MD
LG